Rikicin Jigawa: ‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane tara  

Jigawa map

 

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane tara da jikkatar wasu hudu sakamakon rikicin kabilanci a kauyen Gululu da ke Karamar Hukumar Miga a ranar Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar, SP Shi’isu Adam, ya ce rikicin ya fara ne bayan wasu da ake zargin Fulani sun saci hibiscus da wasu kaya daga wani shago.

Mutanen kauyen sun bi sawunsu zuwa sansanin Fulani a Yankunama, Jahun LGA, inda aka ce Fulani sun fara kai musu hari da baka da kibau, suka kuma jiwa mutane hudu rauni.

Lamarin ya kazanta bayan mutanen kauyen sun mayar da martani, suka kona gidaje a wurare daban-daban a Miga da Jahun.

‘Yan sanda sun isa wajen don dawo da zaman lafiya, inda suka gano gawarwaki tara. Jami’an lafiya sun tabbatar da mutuwar su.

Shugabannin al’umma da kungiyoyi sun yi taro don hana kara tabarbarewar lamarin.

Rundunar ‘yan sanda ta ce an kwantar da rikicin, kuma ana ci gaba da bincike don kamo masu hannu a rikicin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here