Shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya jinjina wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewarsa da jagoranci mai tausayi, yayin da yake cika shekaru 62 a duniya.
Kwankwaso ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya yabawa Yusuf kan nasarorin da ya samu a cikin watanni 19 da ya yi a mulki, yana cewa ya kawo sauye-sauye masu amfani ga rayuwar al’ummar Kano.
Ya kuma bayyana Yusuf a matsayin mutum mai biyayya da kwazon shugabanci, tare da yin fatan Allah ya kara masa karfin gwiwa da hikima don ci gaba da yi wa al’umma hidima.