Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabbin nade-nade domin karfafa ayyukan gwamnatinsa.
Sanarwa daga mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta bayyana cewa daga cikin sabbin nade-naden akwai nadin Hon. Ahmad Muhammad Speaker a matsayin Mai Bawa Gwamna Shawara kan Harkokin Yada Labarai, da Injiniya Ahmad a matsayin Mai Bawa Shawara kan Ayyuka.
Haka nan, Malam Sani Abdullahi Tofa an nada shi a matsayin Mai Bawa Gwamna Shawara kan Harkokin Musamman, yayin da aka nada Hon. Ibrahim Jibrin Fagge da Hajiya Ladidi Ibrahim Garko a matsayin Shugabannin Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi da Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikatan Jihar Kano.
Za a yi bikin rantsar da sabbin kwamishinoni da masu ba da shawara a ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025, a Fadar Gwamnatin Kano.