Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi tsokaci kan gayyatar da Kamfanin NNPCL ya yi masa don ziyarar matatun mai na Fatakwal da Warri, yana mai cewa hakan rashin girmamawa ne.
Ta bakin mai magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi, Obasanjo ya ce babu wata wasika ta gayyata da aka aiko masa, kuma hanya irin wannan ba ta dace da mutuncin ofishinsa ba.
A wata hira da ya yi a tashar Channels, Obasanjo ya bayyana yadda gwamnatin sa ta nemi ƙungiyoyi masu zaman kansu kamar Shell da Dangote su gudanar da matatun mai, amma aka ƙi wannan yunkuri bayan shi ya bar mulki
Ya kuma ce an kashe sama da dala biliyan biyu kan matatun, amma har yanzu ba sa aiki yadda ya kamata.
Sai dai kakakin NNPCL, Femi Soneye, ya kare matsayinsu, yana mai cewa an gyara matatun domin su zama na zamani, kuma sun gayyaci Obasanjo ya gani da idonsa.