Yan sanda sun karyata zargin da wani malamin jami’a yayi game da ma’aikacinsu 

Fake News 750x430

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta musanta zargin da Adamu Garba Zango, wani malami a Jami’ar Baze, ya yi cewa wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Jihar Kaduna yana siyar da makamai ga ‘yan ta’adda.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a X (Twitter), an bayyana cewa hoton da aka yada yana nuna Kingsley Udoyen, wani mutum da aka kama a Akwa Ibom a shekarar 2019 saboda kwaikwayon matsayin jami’in ‘yan sanda.

Rundunar ta ce babu wata alaka tsakanin rundunar ‘yan sandan Kaduna da zargin, tare da gargadin cewa yada labaran karya ya saba wa dokokin “bata suna da laifukan” yanar gizo.

‘Yan sanda sun bukaci ‘yan kasa su dogara da sahihan hanyoyin sadarwar hukuma don samun bayanai daidai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here