Hanifa: A shirye nake na sanya hannu kan hukuncin kisa-Ganduje

9E72BF30 1D30 4423 A841 B9C141498AE2
9E72BF30 1D30 4423 A841 B9C141498AE2

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin sanya hannu kan hukunci ga wanda ya yi wa Hanifa Abubukar ‘yar shekara 5 kisan gilla, matukar kotu ta yanke wannan hukuncin.

Gwamna Ganduje Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin Kano zuwa gidansu Hanifa domin yi musu ta’aziyya. Yayin ziyarar ya kasance tare da mataimakinsa, Alhaji Nasuru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari da sauran manyan jami’an gwamnati.

Bayanin hakan na kunshe ne cikim wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Gwamna Ganduje, Malam Abba Anwar aikowa da Solacebase a yammacin litinin.

“Muna da kwakkwaran tabbaci daga kotun da ke tafiyar da lamarin cewa, za a yi adalci. Zamu tsaya domin tabbatar da hakan. ” in ji sanarwar.

Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa, “Duk wanda aka samu da wannan danyen aiki, shima zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba.”

Gwamna Ganduje ya ce “Tsarin mulkin mu ya tanadi cewa idan aka yanke hukuncin kisa, tsarin mulki ya bawa gwamna damar bayar  izinin aiwatar da hukuncin kisa. Don haka nake tabbatar muku da cewa kara koda dakika daya ba wajen sanya hannu.”

Gwamnan na jihar Kano Ya kara da cewa, “gwamnati za ta kula da iyalan marigayiya Hanifa, yana bayyana cewa gwamnati za ta yi wani abu kan  makarantun da wannan bala’i ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here