Sama da maniyata 940 zasu iya rasa aikin Hajjin bana a Kano

NAHCON NEW 750x430 1
NAHCON NEW 750x430 1

Sama da maniyata  940 za su iya rasa aikin Hajjin bana a Kano, wanda ya rage saura awanni kadan a fara aikin Hajjin, sakamakon rashin jiragen da zai kwashe su zuwa Saudiya.

Yayin da yake zantawa da jaridar Solacebase yau da safe, sakataren hukumar walwalawar alhazai ta jihar Kano, Muhammad Abba Danbatta, ya ce abin bakin cikine a ce hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, ta kasa cika alkawarin da akai da ita na kwashe alhazai kwana biyu da suka wuce.

Danbatta ya kara da cewa da safitar yau, kamfanin jirgin AZMAN wanda yake da kujerun mutum 400, amma kawai alhazai 250 ya dauka, inda ya bar alhzai 940 a kasa.

“NAHCON ta yi mana alkawari kwana biyu da suka wuce, cewa zata kawo jiragen da zasu iya kwashe duk alhazan jihar Kano, amma ta kasa cika alkwarain da ta dauka”

“jirgin AZMAN yayi jigila 6 kadai, inda ya kwashe alhazai 1,175, saboda kwaramin jigin suke amfani dashi ba zai dauki alhazai masu yawa ba”

“ shi’isa muka kai korafin mu ga hukumar alhazai ta kasa, don su yi duba ga yawan alhazan da muke dasu a jihar Kano, ta bamu jirgin Max Air ya yi jigilar alhazan mu”

Danbatta ya kara da cewa yaje Abuja ya fi sau goma akan matsalar, sannan sun tura wasika sama da 11 zuwa hukumar ta NAHCON, sannan gwamna da kan sa, shima ya aike musa da wasika sama da guda 3, don su bamu jirgen Max Air, don gudun faruwar halin da muke ciki a yanzu.

“gaskiya ina cikin bakin ciki akan wananna matsalar, amma ina fata maniyatan bazasu rasa aikin Hajjin bana ba”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here