Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Saudiya, GACA, ta amince da tsawaita wa’adin sauka a filayen jiragen ta ga masu jigilar alhazan Najeriya.
Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta fitar, NAHCON ta ce Saudiya ta amunci da kara wa’adin ne biyo bayan Alhazai 3000 na Najeriya da basu sami damar tashiba.
Sanarwar ta kuma kara da cewa an kara wa adin ne bayan tau-tau nawa da Najeriya tayi da kasar Saudiya, wacce Alh Zikrullah Hassan, ya jagoranta a kasar Saudiya.
A cikin sanarwar NAHCON ta ce kara wadin zai bawa kamfanin jirgin Max Air da kuma ta kwaran sa na Azman su cigaba da jigilar Alhazai.












































