Gwamnatin tarayya ta sanya Mutum dubu 98 cikin shirin bada lamuni na GEEP 2.0

Hajiya Sadiya Umar Farouq 678x381 1
Hajiya Sadiya Umar Farouq 678x381 1

Ma’aikatar kare afkuwar ibtila’i, Jin kai da walwalar Jama’a ta kasa ta kammala shirin fara wani shirin Gwamnati na bada lamuni domin bunkasa sana’o’i da harkokin noma a Jihohi 36 na fadin kasar nan ciki har da birnin Tarayya Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan da aka kammala tantancewa tare da zabar wadanda suka nemi lamunin a karon farko suka kuma cancanta a basu bashin kudi daya kama daga Naira 50,000 zuwa Naira 300,000.

Ministar Ma’aikatar Hajiya Sadiya Umar Farouq, tace dukkan wadanda suka cancanta aka kuma zabe su zasu amfana a karkashin shirin na GEEP 2.0, za a fara tura musu sakonnin taya murna a yan kwanaki masu zuwa, domin sanar da su an zabe su tare da kara tabbatar mu su cewa ba kyauta bane bashi ne kudin da za a basu.

“Dukkan wadanda suka cancanta su sani wannan shirin na GEEP 2.0 shiri ne na bada lamuni ba kyauta ba, kuma babu ruwa a ciki yadda aka bawa mutum haka zai maido da shi”. Inji Ministar.

Ministar ta kara da cewa sun gama shirin fara gabatar da tsarin a fadin Najeriya, haka kuma za a fara daukar bayanan wadanda suka cancanta.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Shirin bada lamuni na GEEP 2.0 shiri ne da gwamnatin tarayya ta bullo da shi domin samar da jari ga masu karamin karfi da masu bukata ta musamman da kuma masu kananan sana’o’in da tattalin arzikin su ya samu koma baya, haka kuma tsarin ya kasu zuwa gida uku da suka gadar da: MarketMoni da TraderMoni da kuma FarmerMoni.

TraderMoni tsari ne da za a bada lamuni ga matasa ‘Yan Najeriya dake tsakanin shekaru 18 zuwa 40, da ya kai Naira 50,000, yayin da shi kuma tsarin MarketMoni manufarsa shi ne bayar da bashi ga mata masu karamin karfi da suka hadar Zawarawa da kuma wadanda mazajensu suka mutu, wadanda ke tsakanin shekaru 18 zuwa 55, suma bashi ne babu ruwa da ya kai Naira 50,000 kuma za a biya ne cikin watanni 6 zuwa 9.

Tsarin FarmerMoni shi kuma na Manoma ne dake tsakanin shekaru 18 zuwa 55 musamman a yankunan Karkara, za a basu lamunin kudin da ya kai Naira 300,000 wannan tsari shi kuma ana sa ran duk wanda ya samu shiga zai biya cikin watanni 12 ciki har da watanni 3 na gudanar da aikin Noman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here