Sojojin Runduna ta 3 ta Sojin Ƙasa sun ceto mutane takwas cikin goma da ake zargin ‘yan ta’adda sun sace a wani wurin biki ranar Laraba a Dabawa, Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano.
Wata majiya daga Hedikwatar Sojin Ƙasa ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa wasu ‘yan bindiga da adadinsu ba a tabbatar ba, sanye da kayan sojoji, sun kai farmaki wurin bikin tare da yin awon gaba da mutanen.
Ta ce sojojin da ke sintiri a wani shiri na kwanton bauna a kan layin Kogin Yankwada sun yi gaggawar isa yankin bayan samun rahoton kiran gaggawa, inda suka yi artabu da maharan a Garu Village da ke Jihar Katsina makwabta.
An bi sahun ‘yan bindigar har zuwa hanyar Katsina–Gidan Mutum Daya kafin aka rasa mu’amala da su.
A yayin aikin, an ceto ‘yan mata takwas daga cikin wadanda aka sace, kuma an riga an mayar da su ga iyalansu, yayin da ake ci gaba da kokarin gano da kubutar da sauran mutane biyu.
Majiyar ta ce ana ci gaba da gudanar da atisayen tsaro a yankin domin tabbatar da dawowar sauran wadanda aka sace da kuma hana sake kai hare-hare.













































