Barazanar Trump: Muna sa ido kan halin da ake ciki a Najeriya – Rasha

Vladimir Putin 750x430
Russian President Vladimir Putin speaks during a joint news conference with Belarusian President Alexander Lukashenko following their talks at the Grand Kremlin Palace in Moscow, Russia, Thursday, March 13, 2025. (AP Photo/Alexander Zemlianichenko)

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana cewa ƙasarta tana bin diddigin ci gaban lamarin da ke tattare da rahotannin yiwuwar harin sojin Amurka a Najeriya.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Maria Zakharova, ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Moscow, inda ta bukaci Amurka da ta kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa wajen mu’amala da kasashen duniya.

Zakharova ta ce Rasha tana lura da al’amarin sosai, tare da kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su bi ƙa’idodin doka da tsarin ƙasa da ƙasa wajen warware irin waɗannan batutuwa.

Tun a ranar ɗaya ga watan Nuwamba, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya bai wa ma’aikatar tsaron ƙasar umarni da ta shirya tsare-tsaren yiwuwar ɗaukar matakin soja a Najeriya, domin kare mabiya addinin Kirista daga hare-haren ta’addanci.

Zakharova ta kuma nuna damuwa matuƙa kan labaran take dokar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi a yankin iyakar Lebanon, tana mai cewa Rasha na ci gaba da tattaunawa da ɓangarorin biyu domin kauce wa sake tayar da rikici.

Ta ce ƙasarta za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulɗa na yankin da na duniya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Lebanon da gabashin tsakiyar duniya gaba ɗaya, a cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasa

NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here