Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙunccin Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a ranar Juma’a.
Sultan ɗin, wanda shi ne shugaban majalisar ƙoli ta addinin musulmai a Najeriya, ya gana da shugaban ƙasa cikin sirri don tattaunawa kan batutuwa masu nasaba da ci gaban ƙasa da fahimtar juna tsakanin mabanbanta addinai.
Ziyarar ta biyo bayan wata ganawa da shugaba Tinubu ya yi da babban limamin Katolika na Abuja, Archbishop Ignatius Kaigama, domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin addinai.
Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanai na tattaunawar ba, sai dai rahotanni sun ce ganawar ta mai da hankali ne kan yadda za a ƙarfafa fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma tabbatar da haɗin kai da cigaban ƙasa.
Ganawar ta kuma zo ne a daidai lokacin da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar mataki kan Najeriya saboda zargin take hakkin Kiristoci a ƙasar.
Daga bisani, Sultan ya halarci sallar Juma’a tare da shugaban ƙasa a masallacin fadar gwamnati, inda limamin masallacin, Alhaji Abdulwaheed Abubakar, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su mara wa gwamnati baya wajen aiwatar da shirye-shiryenta na zaman lafiya da tsaro.
Ya jaddada cewa zaman lafiya shi ne muhimmin ginshiƙi ne ga ci gaban mutum da ƙasa baki ɗay.
NAN.













































