Dalilin da ya sa muka dakatar da tantaceGarba Ramat a matsayin shugaban NERC – Majalisar Dattawa

Abdullahi Ramat 677x430

Majalisar dattawa ta bayyana dalilan da suka sa ta dakatar da tabbatar da nadin injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa NERC, wanda ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi na cin hanci domin hana tabbatar da nadin nasa.

Tun a baya dai an tuna cewa tsohon mai ba mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo shawara na musamman, Alwan Hassan, ya yi zargin cewa shugabannin majalisar dattawa a zango na goma sun karɓi cin hancin dala miliyan goma domin dakatar da tabbatar da Ramat a matsayin shugaban hukumar.

Sai dai majalisar dattawa ta musanta wannan zargi, inda ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin rahoton da ake yadawa.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan.

Ya ce majalisar ta ɗauki matakin ne bisa wasu dalilai da suka shafi tsarin gudanar da bincike da tabbatar da cancantar wanda aka naɗa, ba wai saboda wani abin da ya shafi cin hanci ba.Qs

Haka kuma, ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da aiwatar da duk wani bincike cikin gaskiya da bin doka domin tabbatar da cewa wanda za a naɗa yana da cikakkiyar cancanta.

Ya ƙara da cewa majalisar tana nan daram wajen kare amincewar jama’a da tabbatar da gaskiya a dukkan matakan gudanar da ayyukanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here