Buhari zai tafi Belgium a yau Talata

22929F6A C5F3 4EAE 951A 1B2435142986
22929F6A C5F3 4EAE 951A 1B2435142986

A yau Talata ne ake sa ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Brussels babban birnin kasar Belgium domin  halartar taron haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar African Union (AU) da European Union (EU).

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar fadar Shugaban kasa.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai tattauna da Shugabannin wasu kasashe domin ganin yadda zasu tallafawa Nigeria ta bangarori daban-daban.

A cewar sanarwar abubuwan da shugabannin za su tattauna sun haɗa da batun ilimi da sauyin yanayi da makamashi da zaman lafiya da harkokin mulki da harkokin tattalin arziki.

Sanarwar ta ce taron zai gudana daga 17 zuwa 18 na Fabarairu, inda shugabannin nahiyar Africa dana nahiyar Turai za su tattauna kan matsalolin dake addabar nahiyoyin.

Ana sa ran Buhari zai koma gida Nigeria ranar Asabar, bayan kammala taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here