Mutanen da ke cin riba daga rashin tsaro ba za su bar ta’addanci ya kare ba — Masanin tsaro

IMG 20260626 WA0481 595x430

Wani jami’in soji mai ritaya kuma kwarren masanin tsaro, Aminu Hassan Soja, ya ce akwai mutanen da ke amfana daga rashin tsaro da ya dade a Najeriya, wanda hakan ke sa da wahala a kawo karshen ta’addancin ‘yan fashi daji, ‘yan Boko Haram da sauran matsalolin tsaro a fadin kasar.

Da yake jawabi a wani shiri na musamman na SolaceBase TV, Soja ya ce Najeriya tana da karfi da kayan aikin da ake bukata domin yakar kungiyoyin masu aikata laifi, amma wasu da ke cin riba daga matsalar rashin tsaro sun sa ya zama kasuwanci mai riba sosai.

A cewarsa, karuwar kudin fansa da ‘yan fashi ke nema shaida ce cewa satar mutane ta zama kasuwancin laifi mai riba.

“A yau, ‘yan fashi suna neman tsakanin Naira miliyan 50 zuwa miliyan 100 a matsayin fansa. Wannan ya nuna yadda harkar ta zama mai riba a gare su,” in ji shi.

Jami’in sojin da ya yi ritaya ya soki tattaunawa da ‘yan fashi a matsayin dabara mai amfani, yana mai cewa irin wadannan yarjejeniya kawai na samar da sauki na dan lokaci ne sannan suna ba da dama ga ‘yan ta’addan su sake haduwa su ci gaba da ayyukansu a wani wuri.

“Ban taba amincewa da tattaunawa da ‘yan fashi ba, ko da ka tattauna da su, za su koma aikata laifi. Mun ga mutane da yawa da ake cewa sun tuba daga Boko Haram daga baya suka koma daji suna ci gaba da kashe marasa laifi,” in ji shi.

Ya bayyana cewa bayan sun yi yarjejeniya a wani yanki, ‘yan ta’addan suna koma wani yanki ne kawai su ci gaba da kai hare-hare da karbar kudi.

“Saboda haka abin da ke faruwa shi ne, da zarar sun tattauna a wani kauye, sai su koma wani su ci gaba da ayyukansu, a haka suke samun kuɗi mai yawa.”

Soja ya kara da cewa tattaunawar da aka yi da ‘yan fashi a Jihar Katsina a baya ya haifar da yaduwar ‘yan fashin zuwa makwabtan jihohi kamar Kano , ya jaddada bukatar hukumomin Kano su kara karfafa matakan tsaro don hana su kara shiga.

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakai masu tsauri da tsayar da lokaci ga jami’an soji na yaki da kungiyoyin da ke dauke da makamai maimakon barin yakin ya dade.

“Gwamnati dole ta dauki wannan yaki da muhimmanci, ya kamata ta sake tsara dabarun ta, ta tsara shiri mai kyau ta kuma kawar da wadannan masu aikata laifukan cikin dan gajeren lokaci maimakon tsawaita yakin.”

Ya ce, ya kamata jami’an tsaro su dinga kai hari kai tsaye ga ‘yan fashin maimakon su jira su kai hari daga gare su kafin su mayar da martani.

Ya kuma soki jinkirin da sojoji ke yi wajen mayar da martani, inda ya ambaci mutuwar Janar Rabe Abubakar a hannun ‘yan fashi a matsayin misali.

“Abin takaici ne sojoji da suka yi jinkirin kai hari har aka kashe Rabe kafin su fara kai hari. Wadannan masu laifin suna aiki ne a cikin kasarmu. Sojoji za su iya kewaye dazukan da suke boya su kai musu hari mai tsauri,” in ji Soja.

Ya ce daukar mataki mai tsauri, inganta dabarun yaki da ci gaba da kai hare-haren soji su ne muhimman abubuwa don dawo da zaman lafiya da kawo kaarshen rashin tsaro a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here