Fitaccen mawaki Davido ya rabawa gidajen marayu 292 Naira miliyan 250

C1F3EB21 9A98 462A B6B7 F24ACBBFEC84
C1F3EB21 9A98 462A B6B7 F24ACBBFEC84

Fitaccen mawakin nan na Nigeria Davido,  ya cika alkawarinsa ta hanyar raba kyautar Naira miliyan 250 ga zababbun gidajen marayu a fadin kasar nan.

Mawakin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta shafin sa na Twitter a daren ranar Talata.

Davido ya ba da sabuntawa da sunayen gidajen marayun da suka ci gajiyar karimcin nasa.

Davido ya gode wa kwamitin da ya kafa don aiwatar da aikin don gudanar da aiki mai kyau, yana mai cewa “kwamiti ne na mutane masu kima da kishin kasa” wadanda suka sadaukar da lokacinsu don tabbatar da an yi aikin.

Da yake yaba wa magoya bayansa, danginsa da abokansa, Davido ya ce mun tashi ne ta hanyar daukaka wasu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa a watan Nuwambar 2021, mawakin ya bukaci abokansa da su ba shi kyautar Naira miliyan 1 kowannen su gabanin zagayowar ranar haihuwar sa.

An ba shi kyautar Naira miliyan 200 cikin kasa da sa’o’i 48 kuma Davido ya yanke shawarar bayar da kudin ga gidajen marayu a fadin kasar nan. Davido ya kara Naira miliyan 50 daga cikin jakarsa ya zama Naira miliyan 250.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here