NNPP ta yi watsi da yunkurin Amurka na kakaba wa Kwankwaso takunkumi, ta ce batanci ne kawai

Rabiu Kwankwaso

Jam’iyyar NNPP ta bayyana kaduwarta kan rahotannin da ke cewa Majalisar Dokokin Amurka na duba wani kudiri mai suna Dokar ‘Yancin Addini da Daukar Mataki kan Najeriya ta 2026 (HR 7457), inda aka ambaci jagoran jam’iyyar na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders da Fulani Ethnic Militia, a matsayin wadanda za su fuskanci takunkumi da suka hada da hana biza da daskarar da kadarori.

Wannan ya biyo bayan zargin alhakin take hakkin ‘yancin addini mai tsanani.

NNPP ta bayyana shirin kakaba wa jagoranta takunkumi a matsayin batanci.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya fitar ranar Laraba.

Jam’iyyar ta yi watsi da duk wata alaka da ake kokarin dangantawa da Kwankwaso da take hakkin ‘yancin addini

Johnson ya ce watanni kafin wannan lamari, Kwankwaso ya mayar da martani kan matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sake ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matukar damuwa kan zargin tsanantawar addini.

Ya ce a lokacin, Kwankwaso ya yi gargadi kan abin da ya kira saukaka bayanin matsalolin cikin gida na Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta wadda ke fuskantar barazana iri-iri daga masu aikata laifuka a sassa daban-daban na kasar.

Jam’iyyar ta kuma kare tarihin Kwankwaso a matsayinsa na gwamnan Kano, tana mai cewa ya tabbatar an kawar da kungiyar Boko Haram daga jihar, sannan alakarsa da shugabannin Kiristoci a Kano da fadin kasar na nuna kwarewarsa a matsayin jagora na kasa.

Ta kara da cewa lokacin da aka matsa masa lamba kan aiwatar da Shari’a, har ya rasa zabe saboda yawancin masu kada kuri’a Musulmi sun hukunta shi kan goyon bayan dan takarar shugaban kasa Kirista, Cif Olusegun Obasanjo.

Haka kuma a zaben shugaban kasa na 2023, ya yi takara tare da Bishop Isaac Idahosa a matsayin abokin takararsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here