Ƙungiyar ƴan Jarida ta kai ƙorafi ga NCC kan katsewar intanet na watanni uku a Zamfara

NUJ New (1)

Ƙungiyar ƴan Jarida ta ƙasa (NUJ) ta rubuta ƙorafi ga hukumar kula da sadarwa ta ƙasa (NCC) kan matsalar katsewar intanet da ta shafi yankin Zamfara ta Arewa na tsawon watanni uku.

A wata wasika da aka rubuta wa shugaban NCC, Dakta Aminu Maida, a ranar Asabar, Sakatare na shiyyar NUJ Zone A, Abdulrazak Bello Kaura, ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki, da ya shafi kananan hukumomi huɗu da suka haɗar da Birnin Magaji, Kaura Namoda, Shinkafi da Zurmi, inda aka dakatar da sabis na MTN, Airtel da Glo.

Ƙaura ya ce yankunan da abin ya shafa, masu yawan jama’a fiye da miliyan 1.78, sun shiga cikin matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa, inda kasuwanci suka durƙushe, makarantu ke fuskantar cikas, matasa kuma suka rasa damar yin amfani da hanyoyin sadarwar zamani.

Karin karatu: NCC ta umarci kamfanoni su riƙa sanarwa kafin samun matsalar Network

Ya bayyana cewa Zamfara ta Arewa na da matasa masu basira da ƙwarewa a harkokin kasuwanci na zamani, amma katsewar intanet ɗin ya durƙusar da harkokin su, ya katse ilimi, ya haifar da rashin aikin yi da ƙaura, lamarin da zai iya haifar da ƙarin matsalolin tsaro da rikice-rikicen zamantakewa.

Ya kuma nuna damuwa cewa rashin aikin yi na iya jefa matasa cikin sauƙin shiga harkokin ta’addanci ko ƙungiyoyin assha, abin da zai ƙara ta’azzara yanayin tsaro a jihar.

Sakatare Kaura ya yi nuni da dokar sadarwa ta Najeriya ta 2003, yana mai zargin kamfanonin sadarwa da gazawa wajen bayyana wa kwastomominsu dalilin katsewar, tare da kira ga NCC da ta yi amfani da ikon ta wajen tilasta musu bin doka.

Ya roƙi hukumar ta tilasta masu ba da sabis su dawo da intanet a yankin nan da nan, su biya diyya ga kwastomomin da aka rufe, sannan su tabbatar da bin ka’ida ta sanar da abokan ciniki kafin a katse sabis.

Kaura, wanda shi ne Sakatare na NUJ Zone A da kuma shugaban ƙungiyar tsoffin ɗaliban Polytechnic Kaura Namoda, ya jaddada cewa Zamfara ta Arewa na daga cikin yankuna masu saurin bunƙasa a Najeriya, don haka ba za a bar ta baya a fannin tattalin arzikin dijital ba. Ya nemi NCC ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin dawo da amincewar jama’a da kuma tabbatar da adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here