Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada sabbabin masu bashi shawara goma.
Hakan na ciki sanawar da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fita ranar Litinin.
Ya ce sababbin masu bawa gwamnan shawara sune
1. Hon. Garba Dirbunde, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi
2. Hon. Wakili Aliyu Garko, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasashen waje
3. Air Commodore Yusha’u Salisu Tudunwada Wada, Rtd. Mai ba da shawara na musamman, akan harkar Tsaro.
4. Hon. Musa Ado Tsamiya, mai ba da shawara na musamman, kan Magudanan ruwa
5. Gwani Musa Falaki, mai ba da shawara na musamman kan harkokin addini II
6. Dr. Sulaiman Wali Sani, mai ba da shawara na musamman kan harkokin ma’aikatan gwamnati.
7. Farfesa Auwalu Arzai, mai ba da shawara na musamman kan ilimi mai zurfi.
8. Hon. Ahmad Sawaba, mai ba da shawara na musamman kan kula da namun daji.
9. Alh. Tajuddeen Gambo, mai ba da shawara na musamman kan ilimi.
10. Hon. Baba Abubakar Umar, mai ba da shawara na musamman na makarantu masu zaman kansu da na sa kai.
Gwamanan yace an nadasu ne bisa chanchanta, aminci da jajircewa wajen yiwa mutanen jihar Kano hidima.













































