Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Bauchi ta ce kimanin makarantu 79 a karamar hukumar Misau da ke jihar malami daya ne kowanne da ke koyar da dukkan darussa.
Darakta mai kula da harkokin makarantu na hukumar, Korijo Usman, ce ta bayyana hakan a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a karshen mako.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ne ya shirya taron kan shirin shigar yaran da ba sa zuwa makaranta a kananan hukumomin Misau da Alkaleri.
Usman wadda ta yi jawabi a babbar makarantar firamare ta Misau, ya ce yawancin makarantu a yankin da kuma fadin jihar ba su da isassun malaman da za su koyar da yara.
“A Misau akwai makarantu 79 da kowannensu ke da malami daya yayin da babu malamai awasu ko kuma dai ba su isa ba.
“A nan makarantar nan (Misau Central Primary School), suna da dalibai 1,726 da malamai 24. Idan ka yi lissafin za ka ga cewa mafi karancin ma’aunin malami da na dalibai shi ne 45 kuma za ka ga ba mu da shi a Najeriya.
“Idan ka je birnin Bauchi, za ka ga akwai ajujuwa masu dalibai 150 ko 200, har ma da dalibai 220 da 250 da malami daya kacal.
A nasa jawabin sakataren ilimi na hukumar ilimi ta karamar hukumar Misau, Alhaji Abdu, da aka tambaye shi game da rashin isassun malamai a makarantar, ya ce halin da ake ciki a makarantar firamare ta Misau ta fi sauran makarantun karamar hukumar kyau.
Da aka tambayi Umar ko me suke yi don magance wannan rashin isassun ma’aikata a makarantar da sauran su a fadin jihar, Daraktan Kula da Makarantun Korijo Umar ta ce “SUBEB ba ta daukar malamai aiki.”