Gwamnatin Bauchi ta gano ma’aikatan lafiya na bogi sama da 100, tasha alwashin hukunta su

Bala Mohammed

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta gano sama da ma’aikatan lafiya na bogi 100 a cikin jihar, kuma za ta hukunta su bisa ka’idojin aikin gwamnati.

Shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar Bauchi, Sambo Alkali, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Bauchi ranar Alhamis.

Alkali ya ce duk sunayen waɗanda aka gano za a miƙa su ga gwamna Bala Mohammed domin a dauki matakin da ya dace.

Ya bayyana cewa a wani sabon binciken tantancewa da aka gudanar a manyan cibiyoyin lafiya biyar na jihar, an gano sama da ma’aikatan bogi 100.

Ya ce a halin yanzu gwamnati na ci gaba da shirin magance ƙarancin likitoci ta hanyar tsarin da gwamna ya amince da shi, wanda ya samar da sakamako mai kyau.

Karanta: Gwamnatin tarayya ta fayyace rawar da take takawa a fannin kiwon Lafiya a matakin farko

A karkashin shirin, an ɗauki likitoci fiye da 40 daga matakin manyan kwararru har zuwa likitocin aiki, kuma an rarraba su bisa tsarin bincike da bayanai.

Alkali ya kara da cewa an umarce su da su gudanar da nazari kan gibin da ke cikin tsarin kiwon lafiya domin inganta ayyukan asibitoci.

Haka kuma, gwamna ya bayar da umarni ga kwamitin lafiya na jihar da ya tsara sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya domin jawo kwararru su zo aiki a Bauchi.

Ya ce shirin na nufin daidaita albashin ma’aikatan lafiya na jihar da na gwamnatin tarayya, inda aikin ya kusa kammala kuma za a miƙa shi ga gwamna domin aiwatarwa.

A nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar, Muhammed Dambam, ya ce gwamna ya nuna kudirin yin aiki tare da hukumomi da abokan hulɗa wajen rage matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara.

Dambam ya kuma ce gwamnati ta kuduri aniyar inganta asusun magunguna da kayan asibiti ta hanyar ƙarin jarin Naira miliyan 250 a bana, kamar yadda aka yi a shekarar 2024.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here