Darakta Janar na Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Yusuf Bichi, ya ce hukumar ta cire wani dan jarida, Lanre Arogundade, daga jerin sunayen wadanda hukumar ke sanya ido akan su tsawon shekaru 38.
Bichi ya bayyana haka ne a lokacin da wata tawaga daga cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa (IPI Nigeria) ta ziyarce shi a Abuja.
Sakataren cibiyar ta IPI, Ahmed Shekarau, a wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, ya ce ziyarar wani bangare ne na ayyukan da kungiyar ke gudanarwa kan kare lafiyar ‘yan jarida da ‘yancin yada labarai a Najeriya.
Shekarau, ya ce a ranar 10 ga watan Fabrairu ne jami’an SSS suka kama Arogundade tare da tsare shi a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, bayan dawowarsa daga birnin Banjul na kasar Gambia.
Da yake magana kan al’amuran da suka sa aka kama dan jaridan a lokacin da ya isa birnin Lagos, Bichi, ya ce hukumar ta yi hakan ne bisa jerin sunayen da ta shafe shekaru da dama tana sanya idanu akansu, inda hukumar ta bukaci a rika yi wa Arogundade tambayoyi a duk lokacin da ya dawo daga kasar waje.
Ya ce an sanya dan jaridar cikin jerin sunayen ne tun lokacin yana Shugabantar kungiyar dalibai ta kasa (NANS) a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1985.
Shugaban na DSS ya ce bayan an cire Arogundade da farko an sake samun wani batu na kuskure da ya jawo hukumar yaki da fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) ta bukaci a kara sanya ido akansa.
A cewarsa, hukumar ba ta kama mutane da gangan a filayen jirgin sama, “muna yin hakan ne bisa bukatar wasu hukumomin gwamnati da ke da matsala da mutanen da abin ya shafa”.
Bichi ya jaddada bukatar samar da hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da ma’aikatar.
Ya ce ya zama dole a magance da yawa daga cikin ‘rashin fahimta’, domin manufarsu ita ce wanzar da zaman lafiya a cikin al’umm, inda ya kara da cewa sada zumunci da mu’amula mai kyau da kafafen yada labarai na daga cikin manufar Hukumar.
Tun da farko, shugaban kungiyar ta IPI a Najeriya, Musikilu Mojeed, ya koka da yadda ake ta samun tauye hakkin ‘yan jarida a yayin da suke gudanar da ayyukansu kamar yadda tsarin mulkin kasa ya basu dama.
Mojeed, ya ce dan jarida yana da damar bin hakkin jama’a da kuma dorawa gwamnatoci da daidaikun mutane da kuma hukumomi alhakinsu.
Da yake buga misali da kididdigar ‘Yancin ‘Yan Jaridu ta Duniya da kungiyar ‘yan jarida ba tare da iyaka ba, ta fitar a shekarar 2021, ya koka da yadda Najeriya ta kasance cikin kasashen yammacin Afirka mafi hadari da wahala ga ‘yan jarida.
A cewarsa, ana yawan farmakar ‘yan jaridar leken asiri, ana kuma kama su ba bisa ka’ida ba, ko ma a kashe su.












































