Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, ta umurci hedkwatar Hukumar dake bada lauyoyi ga marasa karfi ta Kasa (wato LACN) da ta bayar da lauyan da zai wakilci Malamin nan na Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, a ci gaba da shari’ar da ake yi kan cin zarafin Ma’aiki.
Kamfanin dillancin Labarai na Kasa NAN ya rawaito cewa gwamnatin jihar Kano ta tuhumi Kabara da laifuffuka guda hudu da suka shafi kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a ranakun 10 ga watan Agusta da 25 ga watan Oktoba da kuma 20 ga watan Disambar shekarar 2019.
Yayin da aka ci gaba da zaman kotun a ranar Alhamis, wanda ake kara ya bayyanawa kotu cewa zai ci gaba da kare kansa a gabanta.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kotun ta ce lauyoyinsa sun mika mata takardar ficewa daga daga shari’ar.
Ko da kotu ta tambayi Abduljabbar din kan ficewar lauyoyinsa daga shari’ar sai ya ce “Ina da masaniyar hakan hasalima ni ne na koresu sakamakon sun saba yarjejeniyar da muka kulla”.
Don haka Malamin yace shi yanzu a kyaleshi zai ci gaba da kare kansa, anan ne mai gabatar da kara ya tashi yace ai a ka’ida ba za’a ci gaba da shari’ar ba tare da Lauya ba.
A ranar Alhamis ne dai aka ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar Kano da Malam Abduljabbar Kabara a babbar kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a kofar kudu karkashin jagorancin mai Sharia Ibrahim Sarki Yola.
Inda Lauya mai gabatar da kara Farfesa Nasir Adamu Aliyu ya jagoranci sauran lauyoyin.
Daga karshe Kotun ta ce a rubuta takarda zuwa ga hukumar dake kula da lauyoyi don su baiwa Abduljabbar din Lauyan da zai kareshi.













































