Zaben 2023: Buhari ya umarci Emefiele da ya sauka daga mukaminsa

President Buhari With CBN Governor Godwin Emefiele
President Buhari With CBN Governor Godwin Emefiele

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci gwamnan babban bankin Kasar CBN Godwin Emefiele, da wadanda ke rike da Ofisoshin Gwamnati kuma suke sha’awar tsayawa takara a zaben shekarar 2023, da su sauka daga mukamansu.

Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a wata takardar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Mustapha ya ce shugaban ya lura da yadda wasu mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da shugabannin ma’aikatu da ministoci ke nuna nuna sha’awa da aniyarsu ta tsayawa takara.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne wata motu ta hana gwamnan babban bankin Godwin Emiefele, tsayawa takarar shugabancin kasar a kowace jam’iyyar siyasa gabanin babban zaben 2023.

Anan me Lauyan Emefiele, Mike Ozekhome ya bukaci kotun da ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya daga hana shi shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya fi so.

Kazalika umarnin ya jaddada cewa duk mai neman takarar kuma yana rike da mukamin siyasa to ya gaggauta ajiye mukaminsa kafin ranar Litinin 16 ga Mayun 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here