A ranar Alhamis din nan ce ake sa ran wata tawagar jigajigan Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da Ministan Kwadago Sanata Chris Ngige, zasu koma teburin tattaunawa da Kungiyar malaman Jami’o’i ta Kasar ASUU.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran ma’aikatar Kwadago ta tarayya Olajide Oshundun, aka kuma rabata ga ‘Yan Jaridu.
Sanarwar tace taron za a gudanar da shi ne tare Mambobin sauran kungiyoyin Kwadago na kasar, da kuma wasu kungiyoyin Sa kai.
Sanarwar ta kara da cewa shugaban Ma’aikatan fadar shugaban Kasa Buhari, Farfesa Agboola Gambari, ne zai jagoranci zaman tattaunawar, inda ake fatan samun maslaha tsakanin bangarorin biyu.













































