Ƙungiyar ƴan fansho ta ƙasa (NUPCPS) ta bayyana damuwa kan cire mambobinta da sauran masu ritaya daga samun damar shiga tsarin inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS).
Sakataren ƙungiyar ƙasa na ƙungiyar, Mista John Bisan, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron wayar da kai na kwana biyu kan tsarin biyan fansho a Lagos ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa cire tsofaffin ma’aikata daga tsarin inshorar lafiya babban zalunci ne da rashin adalci ga tsofaffin ‘yan ƙasa da suka yi wa ƙasar hidima tun suna ƙuruciya.
Ya ce lokacin ritaya shi ne lokacin da tsofaffin ma’aikata ke bukatar amfani da tsarin lafiya sosai, domin yawanci suna fama da rashin lafiya a wannan lokaci.
Bisan ya bayyana cewa, da zarar mutum ya kai shekara 60 ko kuma ya yi ritaya daga aiki, ake cire shi daga tsarin inshorar lafiya, abin da ya kira da rashin adalci da raini ga waɗanda suka sadaukar da shekaru masu yawa wajen bautar ƙasa.
Ya ce, ba daidai ba ne mutum ya yi wa ƙasarsa hidima tsawon shekaru 35, amma daga baya a hana shi samun kulawar lafiya kyauta.
A cewar sa, wannan shi ne lokacin da muke bukatar taimako, domin yawancin tsofaffin ma’aikata suna fama da hauhawar jini, ciwon sukari, da matsalolin zuciya, amma ba su da kuɗin magani ko yin gwaje-gwaje.
Sakataren ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su kula da tsofaffin ma’aikata kamar yadda ake yi a ƙasashen Turai da Amurka, inda tsofaffi ke samun kulawa ta lafiya kyauta.
A nata jawabin, darakta janar na hukumar kula da biyan fansho (PENCOM), Hajiya Omolola Oloworaran, ta bayyana cewa an ƙaddamar da shirin ba da damar samun kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin biyan fansho.
Ta ce wannan shiri na inshorar lafiya yana cikin muhimman manufofi na kare ‘yan fansho da tabbatar da mutuncin su bayan ritaya.













































