Daran-Dam Zaman Jakadan Faransa A Nijar Duk Da Matsin Lamba Na Yafice – Macron

118321 thumb

Shugaba Emanuel Macron na faransa yace zaman Jakadan Faransa a Nijar na nan daran-dam a kasar duk da matsin lamba da sojoji masu juyin mulki a baya-bayan nan sukayi na ya fice daga kasar.

Shugaba Emmanuel Macron a wani jawabi ga jami’an diflomasiyya a ranar Litinin ya jaddada goyon bayan Faransa ga hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum, wanda shawararsa na kin yin murabus da yakira amatsayin jajircewa.

“Ina ganin manufarmu tana kan hanya kuma ta dace. Jajircewar da Shugaba Bazoum, da kuma alkawurran da jakadan mu na kasa ya yi na bisa turba duk da matsin lamba.

Macron ya ce “Duk da sanarwar da hukumomin soji, ba bisa doka suka yi ba.”

A ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata ne dai gwamnatin Nijar da ta kwace mulki a wani juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli, ta ce ta umarci jakadan Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar cikin sa’o’i 48.

Macron ya kuma yi watsi da kiraye-kirayen da wasu daga cikin Amurka da Turai suka yi na cewa kasashen yammacin duniya su yi watsi da shirin Bazoum.

Macron ya ce “Ba mu san wadanda suka aiwatar da shirin ba, muna goyon bayan shugaban da bai yi murabus ba”

Babbar kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka na kokarin tattaunawa da shugabannin juyin mulkin Nijar, kuma ta ce a shirye take ta tura dakaru domin maido da tsarin mulkin kasar idan yunkurin diflomasiyya ya ci tura.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here