DSS Sun Hana Mataimakin Gwamnan Edo Ganin Obaseki

Surprise as security aide denies Edo deputy gov access to Obaseki in Church 750x430
Surprise as security aide denies Edo deputy gov access to Obaseki in Church 750x430

Rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, ya sake ɗaukar sabon salo lokacin da jami’an hukumar DSS suka hana Shaibu ganin gwamnan.

Shaibu yana ɗaya daga cikin baƙin da suka halarci addu’o’in da aka gudanar a coci domin murnar cikar shekara 32 da ƙirƙiro jihar Edo.

A wajen yin addu’o’in wanda aka gudanar a ɗakin taro na Festival Hall a gidan gwamnatin jihar a birnin Benin ranar Lahadi, Shaibu ya je wurin gwamnan domin ya gaida shi, amma sai jami’in DSS ya hana shi.

Obaseki, wanda yake zaune tare da matarsa, Betsy da Charles Aniagwu, kwamishina daga jihar Delta, sai ya kawar da kansa yayin da Shaibu yake ƙoƙarin yi wa jami’an bayani wanda ya ƙi yarda ya bar shi ya ga gwamnan.

Bayan duk ƙoƙarin da mataimakin gwamnan ya yi domin ganin ya ga gwamnan ya ci tura, sai ya haƙura ya koma wajen zamansa.

Da yake magana a kan lamarin, kakakin watsa labaran gwamnan, Andrew Okungbowa, ya bayyana cewa jami’in DSS ɗin aikinsa kawai yake yi.

“Duk abinda ya faru a wajen ba gwamna ba ne ya sanya kuma baya da masaniya kan abin da jami’an tsaron ke yi. A taƙaice jami’an tsaron aikinsu kawai su ke yi. Bayan haka gwamnan bai san cewa mataimakinsa ya zo domin gaida shi ba.”

“Coci waje ne da ake tara mutane, saboda haka jami’an tsaro suna da haƙƙin kare gwamna a wajen.”

Duk da kunyata shi da aka yi, Shaibu ya ƙara tabbatar da cewa har yanzu yana tare da gwamnan kuma a shirye yake ya yi masa biyayya.

Da yake magana da manema labarai a wajen, mataimakin gwamnan ya bayyana Obaseki a matsayin babban yayansa. Shaibu, wanda ya fito daga yankin Edo ta Arewa, yana son ya gaji Obasaki wanda ya fito daga yankin Edo ta Kudu, amma gwamnan yana son magajinsa ya fito daga yankin Esanland na Edo ta Tsakiya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here