2023: Za a mika sakamakon zaben gwamnan Kogi daga rumfunan zabe – INEC

BVAS SABO.jpeg
BVAS SABO.jpeg

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za a mika sakamakon zaben jihar Kogi ranar 11 ga watan Nuwamba ta hanyar lantarki kai tsaye daga rumfunan zabe zuwa  shalkwatar ta.

Kwamishinan Zabe na INEC a Kogi, Farfesa Gabriel Longpet ne ya bayyana hakan a wani taron kwana biyu da manema labarai suka gudanar kan zaben Kogi wanda cibiyar ‘yan jaridu mai zaman kanta, IPC ta shirya a Abuja.

Farfesa Longpet ya ce watsa sakamakon ta hanyar lantarki zai taimaka wajen kawar da magudi, magudin zabe da sauran kura-kurai da kuma tabbatar da an dora gaskiya da gaskiya a harkar zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here