Gwamnatin Jigawa ta hada gwiwa da kungiyar samar da dabino a kasar Saudiyya da kamfanin Netay Agro-Tech mai sana’ar noma a Najeriya domin bunkasa noman dabino a jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki.
Jagoran tawagar, Abdul’aziz Abdurrahman-Al-Awf, ya nanata kudirin kungiyar na kawo sabbin dabarun noma na zamani a Jigawa.
Ya ce, “Muna son tabbatar da samar da dabino a duk shekara, maimakon amfanin gona na yanayi kuma hadin gwiwa da mu zai bada damar horar da manoma da kuma karfafa matasa.
Karin karatu: Gwamnatin Kano da Bankin Duniya sun raba Dala dubu dari 250 ga mazauna yankuna 10 don Noma mai inganci
“Muna kuma son gabatar da wasu nau’in dabino mafi daraja da yawan amfanin gona a kasar Saudiyya da za a noma a Jigawa.”
Babban makasudin ziyarar, in ji shi, ita ce, tuntubar juna bisa dabarun hadin gwiwa don bunkasa noman dabino a Jigawa ta hanyar bunkasar fasahar noma, da musayar fasahohin zamani da zuba jari a fannin noma.
“Wannan hadin gwiwa ba wai kawai zai kara yawan dabino da ake nomawa a Jigawa ba, zai kuma inganta noman, wanda hakan zai sa jihar ta zama cibiyar noman dabino a Najeriya da Afirka,” Ya kara da cewa, Namadi ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa ya dace da tsarin bunkasa noma na jihar.
Ya ce “muna maraba da ku zuwa jihar Jigawa kuma mun yaba da sha’awar ku na yin aiki da mu. A matsayinmu na gwamnati mun jajirce sosai wajen wannan hadin gwiwa domin zai amfani al’ummarmu matuka.













































