Gwamnatin Kano da Bankin Duniya sun raba Dala dubu dari 250 ga mazauna yankuna 10 don noma mai inganci
A wani yunkuri na karfafa yanayi da habaka noma, gwamnatin jihar Kano ta hanyar shirin farfado da ayyukan Noma a jihar (ACRESAL) ta raba wani tallafi ga al’umma a yankuna 10 inda konannen su ya amfana da tallafin dala 25,000 kowannensu.
SolaceBase ta rawaito cewa an ware jimillar Dala dubu dari 250,000 don saka hannun jari a fannin noma da dabarun bunƙasawa da sarrafawa, har ma da inganta kayan Noma.
Karin karatu: Manoma da Makiyaya sun cimma matsayar samar da zaman lafiya a Katsina
Da yake jawabi a wajen taron a ranar Alhamis jami’in ayyukan ACReSAL na Kano kuma Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya jaddada manufar shirin na dakile illolin sauyin yanayi da kuma inganta samar da abinci ta hanyar ayyukan noma mai dorewa.
“Wannan asusu bai tsaya a taimakon kudi kawai ba, akwai dabaru na karfafawa manoma gwiwa, inganta rayuwar al’umma” in ji Dokta Hashim.
Ya ce, an zabo al’ummar yankuna guda 10 da suka ci gajiyar shirin kamar mazauna Chiranchi, Diso, Kofar Naisa, Galadanchi, Gwale, Kwankwaso, Garo, Sarigirin, Gobirawa, da Dala, bisa tsauraran sharudda don tabbatar da rikon amana da jajircewa wajen gudanar da aikin noma mai dorewa.
Don tabbatar da gaskiya da dorewar aikin, an kafa tsarin gudanarwa, gami da kwamitocin Gudanar da Asusun juyawa jarin na Jama’a (CRFMCs), da Wakilan Kasuwancin Al’umma (CBAs), da Kwamitin Amintattu (BoTs).