Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan fashe-fashen da suka faru a wasu sassan Maiduguri a yammacin ranar Litinin.
Zulum, wanda ke halin yanzu a ƙasar Saudiyya domin gudanar da Umra, ya bayyana harin a matsayin abin ƙyama, mai muni da rashin tausayi, wanda aka kai kan mutane marasa laifi a cikin watan Ramadan mai alfarma.
A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar, an bukaci a ƙara sa ido da kuma ƙarfafa matakan tsaro, musamman a wuraren ibada, yayin da ake tunkarar lokacin bukukuwa.
Zulum ya ƙara da cewa yana cikin matuƙar jimami kan fashe-fashen da suka faru a wasu sassan birnin a yammacin ranar Litinin, yana mai cewa tunaninsa da addu’o’insa suna tare da iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma waɗanda suka jikkata sakamakon fashewar.
Ya kuma ce wannan aiki abin Allah-wadai ne ƙwarai, mai tsananin muni da rashin ɗabi’a, yana mai jaddada cewa irin wannan ta’addanci ba shi da gurbi a cikin al’umma.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ƙarin yawaitar hare-haren baya-bayan nan na da alaƙa da tsauraran matakan aikin soji da ake gudanarwa a dajin Sambisa da sauran maɓoyar ‘yan tada ƙayar baya.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro suna kan lamarin, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana sake samun tangardar tsaro a Maiduguri da ma fadin jihar baki ɗaya.
Zulum ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, tare da kai rahoton duk wani motsi ko aiki da suke zargi ga hukumomin tsaro.










































