Ana fargabar mutuwar wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wasu fashe-fashe da suka faru a kusa da kasuwar Monday Market a Maiduguri, jihar Borno, da kuma kusa da wurin tsaro a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.
Rahotanni sun nuna cewa bam ɗin sun fashe a lokaci guda da misalin ƙarfe 7:02 na yammacin ranar Litinin.
Shugaban ayyuka na hukumar kashe gobara ta gwamnatin tarayya a jihar Borno, Mohammed Kafaran, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa tuni hukumar ta tura jami’anta zuwa wurin domin duba halin da ake ciki.
Ya bayyana cewa fashewar ta faru ne a yankin kasuwar Monday Market da ke kusa da Elkanemi, kuma jami’an hukumar suna wurin domin tantance abin da ya faru.
Shaidu sun bayyana cewa an kwashe mutane da dama da suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawa ta likitoci.
Wasu daga cikin shaidun sun ce an ga gawarwaki a ƙasa, yayin da aka garzaya da wasu masu raunuka zuwa asibitin ƙwararru na jiha da ke Maiduguri domin yi musu magani.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yana kan hanyarsa bayan ya bar ofishin gidan waya ne lokacin da ya ji wata ƙara mai ƙarfi ta fashewa.













































