Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno ta tabbatar a ranar Talata cewa mutane 23 sun mutu yayin da 108 suka jikkata a Maiduguri sakamakon fashewar bama-bamai da suka faru a ranar Litinin.
‘Yan sandan sun bayyana cewa ana zargin ‘yan kunar bakin wake ne suka kai hare-haren da misalin ƙarfe 7:24 na yamma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Nahum Daso, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna an aiwatar da fashe-fashen ne ta amfani da na’urorin fashewa da aka ƙera na gida ta hannun waɗanda ake zargin ‘yan kunar bakin wake ne.
Ya ƙara da cewa hare-haren sun faru ne a tsakiyar kasuwar Maiduguri da aka fi sani da kasuwar Monday, ƙofar asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, da kuma yankin gadar sama ta ofishin gidan waya a cikin birnin.
Ya bayyana cewa haɗaɗɗiyar tawaga ta rundunar ‘yan sanda ta musamman, sojoji da sauran jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun gaggauta isa wuraren da lamarin ya shafa domin ɗaukar mataki.
Karanta: Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da tashin abin fashewa a Maiduguri, ya bukaci a kwantar da hankali
Sun kuma tsare wuraren da lamarin ya faru tare da killace su, yayin da sashen kula da bama-bamai da wargaza su na rundunar ‘yan sanda ya gudanar da bincike sosai domin tabbatar da cewa babu wata barazana da ta rage.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Naziru Abdulmajid, ya ziyarci wuraren domin duba halin da ake ciki tare da jajantawa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Rundunar ta tabbatar wa mazauna yankin cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tare da ƙara matakan tsaro domin hana sake faruwar irin wannan lamari.
Ta kuma kwashe waɗanda abin ya shafa ta hannun jami’an agajin gaggawa ciki har da Hukumar kula da agajin gaggawa ta ƙasa da kuma Hukumar kula da agajin gaggawa ta jihar Borno zuwa cibiyoyin lafiya domin samun kulawa.
Ya ƙara da cewa an dawo da zaman lafiya a wuraren da abin ya shafa, yayin da aka tsaurara tsaro a fadin birnin domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari.
Rundunar ta bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu tare da kasancewa cikin shiri, su kuma rika kai rahoton duk wani motsi ko abu da suka zarga ga hukumomin tsaro, tare da jaddada kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.













































