Yan sanda sun umarci a kama duk jami’an da suke rakiyar mutane na musamman na tare da izini ba

Police badge

Rundunar yan sanda a jihar Akwa Ibom sun bayyana cewa za a cafke duk wani dan sanda da aka samu yana rakiyar mutane na musamman da suka haɗar da dan siyasa ko kuma mutanen da ake ɗauka masu muhimmanci ba tare da sahalewar hedikwatar rundunar ba.

Kwamishinan yan sanda Muhammad Baba Azare ya bayyana wannan umarni bayan ganawar tsara dabaru da manyan jami’an rundunar da aka gudanar a Uyo domin karfafa ladabtarwa da tabbatar da tsaron jama’a a fadin jihar.

Ya jaddada cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan sabunta umarni na cikin gida bayan samun karuwar take dokar da babban sufeton yan sanda ya bayar kan hana rakiyar mutanen da ake ɗauka masu muhimmanci da ba su da izini daga hedikwatar rundunar.

Kwamishinan ya bayyana cewa wadanda suka keta umarnin za a kwace bindigoginsu, a gurfanar da su gaban kotun ma’aikata, sannan a hukunta su, tare da dora alhakin ladabtarwar kan kwamandojin yankuna da shugabannin sassa.

Ya kuma jaddada damuwarsa kan yawaitar yada labaran karya da bayanan da ba su da tushe musamman a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankalin jama’a da kuma kawo barazana ga zaman lafiya a jihar.

Don haka aka umurci jami’ai su kara kusantar al’umma da kuma bin diddigin duk wanda ke yada bayanan karya domin gurfanar da su.

Kwamishinan ya tunatar da jami’an kan haramcin tarukan masara dalili da gwamnatin Akwa Ibom ta sanya saboda haka tarukan kan haddasa rikice-rikice, tashin hankali da cikas ga zaman lafiya, inda ya umurci kwamandojin yankuna da sassa na musamman su tabbatar da bin umarnin ba tare da kuskure ba, domin gazawa na iya jawo hukunci.

A bangaren matsalolin tsaro da ke fitowa kamar ƙungiyoyin daba, fashi da makami da kuma kungiyoyin kan titi, Azare ya umurci dukkan sassa da unguwannin rundunar su gudanar da tsare-tsare na binciken kwararru, sintiri, da kuma kai hare-hare na sirri kan wuraren da ake zargin zama mafakar miyagun laifuka, cikin bin doka da nisantar cin zarafi.

Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare Akwa Ibom a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a ƙasar, tare da bukatar jami’ai su kasance masu ladabi, sa ido, da cikakken sadaukarwa ga ayyukansu.

sannan ya bukaci al’umma su kasance masu bin doka tare da bayar da rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin yan sanda mafi kusa domin daukar mataki cikin gaggawa.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta kara hada kai da sauran hukumomin tsaro domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaron jihar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here