Yan Najeriya 82 mata ne ke jiran hukuncin kisa- ASF Faransa

Hanging 0 750x430

Wata kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ASF a Faransa ta bayyana cewa mata ‘yan Najeriya 82 na tsare a gidajen gyaran hali daban-daban a fadin ƙasar suna jiran aiwatar da hukuncin kisa.

Wannan bayani ya fito ne a wani taron horaswa da aka gudanar a Abuja domin karfafa fahimtar matsalolin jinsi a aiwatar da hukuncin kisa.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa taron da ya shafe kwana biyu ana gudanar da shi, kuma an shirya shi ne domin kare haƙƙin matan da ke fuskantar wannan hukunci, a yayin da kungiyoyin kare haƙƙin mata ke gudanar da ranakun fafutukar yaki da cin zarafi.

Daraktar ƙasa ta kungiyar ASF ta Faransa Angela Uzoma-Iwuchukwu ta ce adadin ya daga Najeriya cikin yawan kasashen da ke da mata da suka fi yawa a layin hukuncin kisa a yammacin Afrika.

Ta bayyana cewa wadannan mata suna fama da matsaloli da suka faro tun daga lokacin kamawa, gurfanarwa, har zuwa yadda ake tsare su, inda tsarin shari’a ke nuna bambanci na jinsi.

Ta ce akwai mata da dama da suka sha tashin hankali a gida, kuma lokacin da suka kare kansu lamarin ya rikide ya zama laifi, amma tsarin shari’a ba ya ɗaukar wannan matsayin hujja a kansu.

Ta kara da cewa yawancin matan na fama da talauci wanda ya hana su samun lauya mai inganci da zai kare su yadda ya kamata, wanda hakan kan kai su ga fuskantar hukuncin kisa.

Ta kawo misalin wata baiwar Allah da aka yanke wa hukuncin jifewa da dutse a Jihar Katsina saboda ta samu ciki ba tare da aure ba, inda daga bisani shiga tsakani ya sa kotu ta soke hukuncin.

Ta ce akwai bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin kisa ga waɗannan mata, tare da la’akari da su a matsayin wadanda suka tsira daga cin zarafin cikin gida, musamman idan hakan ya taka rawa wajen kai su ga aikata laifi.

Kungiyar ta jaddada cewa irin wadannan abubuwa ya kamata su zama abin saukaka hukunci a lokutan yanke hukunci.

A nata bangaren, daraktar cibiyar Mothers and Marginalised Advocacy Centre Dr Chioma Kanu ta bayyana cewa kowane fursuna yana da uwa, ko ‘yar’uwa, ko mata ko ‘yarsa da ke jigata saboda rashin adalci a tsarin shari’a.

Ta ce wasu na fama da hukuncin kisa ba tare da samun cikakkiyar shari’a ba, wasu kuma suna tsare ne saboda takardu sun ɓace ko rashin lauya, don haka akwai bukatar tsaurara adalci wajen kare rayuka domin wanda ya mutu ba za a iya dawo da shi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here