Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamitin mutum tara domin binciken zargin biyan albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi 379 da ba a tabbatar da sahihancin bayanansu ba.
Wannan na zuwa ne bayan an gano batun yayin tantance albashi da aka yi ta hanyar raba takardun dummy domin a duba ko bayanan albashi sun dace da na ofis.
Shugaban Ma’aikata na jihar, Alhaji Abdullahi Musa, ya ce kwamitin zai binciki ko ma’aikatan sun yi ritaya, sun mutu ko kuma ba a iya gane su. Za kuma a nemo hanyoyin da za a hana irin wannan matsala a gaba.
Kwamitin na karkashin jagorancin Hajiya Kubra Iman daga Ma’aikatar Al’adu da yawon bude ido, kuma an ba su makonni biyu su kammala binciken.













































