Masu Sana’ar burodi a Kasar nan zasu shiga yajin aiki a ranar Alhamis

Bread 727x430 1
Bread 727x430 1

Wata Kungiyar masu yin burodi karkashin inuwar kungiyar masu sana’ar biredi ta Najeriya (PBAN), sun koka da yadda suke fuskantar hahawar farashin kayayyakin yin buredi a Kasar nan.

A wata sanarwa da shugaban Kungiyar ta PBAN, Emmanuel Onuorah, da jami’in hulda da jama’a na Kungiyar, Babalola Thomas suka fitar tare da sanya hannun hadin gwiwa a ranar Talata, ta ce, tuni sun kammala shirin shiga yajin aikin gargadi daga ranar Alhamis 21 ga watan Yulin shekarar da muke ciki ta 2022 na tsawon kwanaki hudu.

Ta cikin sanarwar Kungiyar ta ce sun dade suna daurewa bisa tunanin cewa farashin kayan zai sauka sai dai har yanzu yana ci gaba da tashi.

“Fulawa ta yi tsada, suga ya yi tsada, man dizel ya yi tsada, mutane da dama sun rufe kamfanoninsu saboda babu riba.”

Sanarwar ta kara da cewa masu sana’ar suna tafka asara hatta uwar kudin da suka zuba a cikinta baya dawowa.

A cewarsu “Duka ‘yan kungiyarmu da ma wadanda ba su cikin kungiyarmu za su shiga wannan yajin aikin.”

Kungiyar ta kuma bukaci hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) da ta yi nazari kan tarar Naira dubu 154,000 da ake tuhumar gidajen biredi kan jinkirin sabunta lasisin gudanar da ayyukan su.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar

Kungiyar ta PBAN, ta kuma bayyana cewa wata kungiyar makamanciyarta ta dade tana ganawa da ma’aikatar kula da masana’antu da kasuwanci da zuba jari ta tarayya Abuja (FMITI) tun daga shekarar 2021, ta bayyana cewa babu wani abu da aka cimma daga wannan fafutikar.

A watan da ya gabata, kungiyar manyan masu yin burodi da masu abinci (AMBCN) ta yi barazanar cewa mambobinta za su janye ayyukansu a fadin kasar saboda wannan matsalolin.

A cikin wata sanarwa da AMCN ta fitar, ta bayyana cewa, farashin fulawa da sikari da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen sana’ar biredi sun yi tashin gwauron zabi fiye da kima ta yadda masu yin biredi da yawa ba za su iya ci gaba da sana’ar ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here