Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta ce an kammala tantance cibiyoyin kiwon lafiya dubu 7 da 250 a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja don karbar tallafin da ake bai wa cibiyoyin kiwon lafiya (wato DFF) ta hanyar Asusun Kula da Lafiya na Kasa (wato BHCPF).
A cewarsa, adadin ya kasance tun lokacin da aka fara aiwatar da Asusun Kula da Lafiya a matakin farko (BHCPF) a shekarar 2019 zuwa yau.
Daraktan dake kula da tsare tsaren Lafiya na hukumar Lafiya a Matakin farko ta Kasa NOHCDA, Dakta Nneka Onu, ita ce ta bayyana hakan yayin kaddamar da rahoto kan shirin aiwatar da ayyuka yadda yakamata na ma’aikatan kiwon lafiya matakin farko a Kasar nan ranar Talata a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa rahoton na daga shekarar 2019 zuwa 2021 ya fito ne daga kungiyoyin ONE Campaign da Kungiyar rajin tabbatar da adalci a ayyukan kiwon lafiya na National Advocates for Health da Kungiyar dake Sanya ido a harkokin Lafiya ta Nigeria Health Watch, da Kuma kungiyoyin bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu ta Public and Private Development Centre (PPDC) da sauransu.
Rahoton ya bibiyi ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya a fadin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja musamman a fannin aiwatar da shirin na BHCPF.
Ya Kuma gabatar da wasu shawarwari masu mahimmanci wadanda za su taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiya ga dukan ‘yan Najeriya.
Onu, ta ce shirin NPHCDA bai da kalubale kwata-kwata.
Inda kuma ta lissafa aikin tantance cibiyoyin kiwon lafiya da aka kammala a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, da kuma kara horar da ma’aikatan lafiya karkashin shirin WDC da aka yi a fadin jihohi 35 da babban birnin tarayya Abuja a matsayin wani bangare na nasarorin da aka samu.
Dangane da yadda ake tafiyar da asusun kuwa, Daraktar ta ce hukumar ta yi amfani da fasahar sadarwa wajen bin diddigin yadda ake fitar da kudaden da kuma yadda ake tafiyar da asusun baki daya. Inda ta bayyana rahoton a matsayin matakin da ya dace.
Dakta Chijioke Kaduru, mamba a kwamitn sanya ido kan cutar Corona, a jawabinsa yayin taron, ya ce samar da isassun kudi za su taimaka wajen tafiyar da harkokin lafiya, ta yadda Yan Najeriya zasu samu dukkan abin da suke bukata.
Kaduru, ya ce ba za su yi watsi da kudaden da ake samu daga matakin jiha ba saboda suna da matukar muhimmanci a fannin kiwon lafiya, ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci a duba yadda ake fitar da kudade da kuma amfani da su a matakin kasa baki daya.

Dakta Phyilis Ogah, wata kwararriya ce kan harkokin kiwon lafiyar al’umma kuma kwararriya kan abinci mai gina jiki ta bayyana cewa, tsari yadda shugabanci ke tafiya na daya daga cikin kalubalen da ke tattare da bayar da kudaden hukumar ta BHCPF a kasar nan.
A cewar Ogah, da a ce an fitar da wadannan kudade idan aka amince da su, da ‘yan Nijeriya sun samu ci gaba ta fuskar kiwon Lafiya.
Shima dai kwamishinan lafiya na jihar Enugu, Dakta Emmanuel Ikechukwu Obi, ya ce an samu nasarar da aka samu a jihar ne sakamakon samar da kyakkyawan yanayi da Kuma tsarin shugabanci mai kyau a jihar.
Obi ya ba da shawarar cewa dole ne a sami wani tsani don fito da sababbin fasahohi na kiwon lafiya wandanda zasu ba da damar tafiyar da harkokin kiwon lafiya cikin sauki.














































