Kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU tace wa’adin makonni biyu da shugaban kasa ya bayar domin warware matsalolin da kungiyar ta gabatar ya yi yawa.
Ga malaman jami’o’i, ba zasu haura fiye da kwanaki biyu ba tare da sun magance matsalolin da suka jefa tsarin jami’o’in gwamnati na kasar cikin yajin aikin da ya tsawaita har zuwa watanni biyar ba.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan ta cikin shirin gidan Talabijin na Channels mai suna Siyasa a yau” ranar Talata a Abuja.
“Makonni biyu sun yi tsayi sosai,” in ji shi. “Batun sake tattaunawa an kammala shi daga bangarorin biyu. abinda muke jira daga kareku shi ne ku dawo ku ce mana ‘kun amince’, hakan ba zai dauki kwana biyu ba. An bayyana mana cewa sun kashe biliyoyin kudi don ciyar da yara a makaranta; shin haka ne, yara nawa kuka ga ana ciyar da su?
Sa’o’i kadan kafin shiga shirin da Osodeke, ya yi, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da Kuma wasu cikin ministocinsa dake da ruwa da tsaki cikin lamarin, inda ya samu bayanai kan yadda ake takun saka tsakanin gwamnati da kungiyoyin jami’o’i ciki har da ASUU.
A wajen taron, Buhari, ya umarci ministan ilimi da ya samar da mafita kan yajin aikin da malaman jami’ar ke ci gaba da yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.
Shugaba Buhari ya kuma umurci Ministan Kwadago da samar da aikin yi Chris Ngige, da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha kan su ma su halarci dukkan tarukan da za a yi domin a gaggauta warware rikicin.
Yayin da shugaban kungiyar ASUU ke kallon matakin da shugaban kasar ya dauka a matsayin abin farin ciki, duk da haka yana da ra’ayin cewa ba da wannan umarni ba sabon abu bane.
Ya yi imanin cewa har yanzu gwamnati ba ta shirya kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in ke yi ba, yana mai jaddada cewa ba ya bukatar wani lokaci mai tsawo irin wannan don magance matsalolin.
Farfesa Osodeke, ya kuma tunawa al’umma cewa a baya ma sai da malaman addini karkashin inuwar kungiyar addinai ta Najeriya (NIREC) suka tsoma baki a rikicin domin samun masalaha, har suka gana da shugaban kasar kan lamarin.

Bayan taron da aka yi a watan Fabarairu, shugaba Buhari ya kafa wani kwamiti na mutum uku domin magance matsalar cikin wata guda, Yan kwamitin da suka hada da shugaban ma’aikatan fadar sa da Chris Ngige da Adamu Adamu.
“Wannan kwamitin bai gayyace mu taro ba sai da muka shiga yajin aikin a watan Mayu. To gashi yanzu kuma sauran kwanaki 12? Idan da gaske muke, kumada gaske muna son magance wannan matsalar, ba za a dauki fiye da kwanaki biyu ba.
“An tattauna dukkan batutuwa, wakilan gwamnati sun gana da ASUU, kuma akwai daftarin yarjejeniyar hadin gwiwa da za a duba a dawo a sanya hannun. Shin wannan ne zai dauki makonni biyu don duba abin da kuka yi shawara? Shugaban ASUU ya tambaya.










































