Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya ce nan gaba kadan zai bayyana kaddarorin da ya mallaka la’akari da sauyin da ya samu a yanzu.
Babban Jami’in Kamfanin Malam Mele Kyari, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai bayan da Shugaban Kasa Buhari ya kaddamar da sabon Kamfanin mai a Fadar Shugaban Kasa, dake Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya rawaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin na NNPC wanda zai yi aiki a matsayin kamfani mai zaman kansa tare da bayyana rarar hannun jari ga wadanda suka zuba jarinsu har miliyan 200.
Dokar Masana’antun Man Fetur (wato PIA) ita ce ta tanadin a sauya NNPC zuwa cikakken kamfani na kasuwanci, a karkashin Dokar Kamfanoni ta Allied Matters (CAMA).
Babban Kamfanin Man na Afirka (NOC) zai kuma tallafa wajen samar da ci gaba mai dorewa ga sauran sassan tattalin arzikin yayin da yake samar da makamashi ga duniya baki daya.
Shugaban kamfanin ya ce za a sauya tsarin kamfanin ta yadda za a samu sakamako mai kyau tare da samun karin kwarewa.
“Dole ne mu cika ka’idojin ayyuka masu kyau a masana’antu, ta fuskar gudanar da mulki da kuma tabbatar da cewa an yi amfani da dukkan ka’idoji”. in ji shi.
Kyari ya ce darajarsa za ta bayyana ta hanyoyi biyu: tabbatar da rabon riba da kuma isar da makamashin da masu hannun jari ke nema.
Ya ce sabon kamfanin yana da damar cimma dukkan ayyukan biyu saboda a yanzu kamfani ne mai ba da damar yin aiki cikin sauri kuma yana iya yanke shawara cikin sauri.
Ya ce ana Kuma sa ran tsakiyar shekarar mai zuwa ta 2023, kamfanin zai kasance yana da tsari da hanyoyin bin diddigin ribar da ake samu ga masu ruwa da tsaki.

Dangane da tallafin mai Kuma, ya ce kamfanin na NNPC Limited ba shi da ta cewa a kai sai dai ya zama batun Kasa.
“Ko menene shawara da manufofin Kasar, NNPC zai yi duk abinda ya dace don isar da darajar kasuwanci ga abokin hulda akan farashin da Kasar take so,” in ji shi.













































