Mutane biyar sun mutu sakamakon cutar amai da gudawa a jihar Kano

Ganduje Sallah baba
Ganduje Sallah baba

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyar sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar, duk da daukar tsauraran matakan kariya don dakile barkewar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, shi ne ya sanar da hakan ranar Talata a wani taron manema labarai a jihar.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Tsanyawa ya ce ko a ranar 16 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki ta 2022 an samu bullar cutar amai da gudawa a karamar hukumar Dambatta da ke jihar wanda aka yi gudanar da bincike cikin gaggawa.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar
Kwamishinan ya kuma godewa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa jajircewarsa wajen samar da isassun ayyukan kiwon lafiya masu inganci ga mutanen jihar domin kawar da barkewar cutar amai da gudawa da kuma sauran cututtuka a fadin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here