Muhammadu Buhari ya umurci ministan ilimi Mallam Adamu Adamu da ya warware matsalar yajin aikin da kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i hudu suka dade suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makwanni biyu.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karbi wasu bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyoyin na jami’o’i da gwamnati.
Shugaba Buhari ya kira taron na ranar Talata ne domin karbar bayanai daga tawagar gwamnati kan yajin aikin da ya dauki tsawon lokaci ana yi. Bayan jin ta bakin masu ruwa da tsaki na hukumomin da abin ya shafa, Buhari ya umurci Ministan Ilimi da ya tabbatar da cewa an warware matsalar cikin makwanni biyu tare da kawo masa bayani.












































