Gwamnatin tarayya ta musanta zargin cewa ta biya mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) rabin albashi a watan Oktoba.
Shugaban sashen yada labarai na ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya Mista Olajide Oshundun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu jiya Asabar a Abuja.
Ta cikin sanarwar yace gwamnatin tarayya taki biyan malaman jami’a cikakken albashinsu ne kasancewar basu yi aikin sauran kwanakin watan ba.
Kazalika ma’aikatar ta yi martani kan kalaman shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar Usman Ɗan-Fodiyo dake Sokoto bisa zargin ministan kwadago da bayar da umarnin biyansu rabin albashi.
Tun da farko kunyar Asuu tace ta janye yajin aiki ne biyo bayan umarnin da kotu ta basu na komawa bakin aiki.













































