A wani bangare na dinke barakar cikin jamiyyar PDP gwamnan jihar SOKOTO Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Jigawa Dakta Sule Lamido da shugaban jamiyyar PDP na kasa Iyorcha Ayu, sun sauka a jihar Bauchi, domin gudanar da wani taro.
Tawagar jagororin jamiyyar sun isa Bauchi ne da yammacin ranar Asabar don tattauna yadda za a warware matsalar rikicin cikin gidan jam’iyar PDP.
A jawabin shugaban jamiyyar na Kasa Iyorcha Ayu, kafin fara tattaunawar yace sun je Bauchi ne don ganawa da gwamna Bala Muhammad Abdulkadir, a matsayinsa na daya cikin mutanan dake baiwa jamiyyar babbar gudunmawa bawai don zamansa gwamna kawai ba.
“Mun zo nan ne domin mu yi muku bayani kan wasu abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar mu, da kuma neman shawarar ku ta hikima domin ba wai kai ne gwamnan Bauchi kadai ba, kai ne jagora a kasar nan.
Da yake mayar da martani, Gwamna Bala Mohammed ya ce shi mamba ne na jam’iyyar kuma ya yi imani da ita, ya kara da cewa “mun tashi ne a bayan jam’iyyar har muka zama abin da muka zama.
“Mun san cewa mun fito ne daga jam’iyyar ANPP (All Nigerian Peoples Party), amma tabbas duk abin da muka zama a wannan jam’iyya ne.
“Mun tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyyar musamman yankina a matsayina na mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa mai kula da shiyyar Arewa.
Kazalika sun tattauna batutuwan da suka shafi batun gangamin yakin neman zaben da ke kara matsowa.













































