Rundunar Yan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da cewa Yan bindiga, sun sako wasu matasa 21 da aka yi garkuwa da su a wata gona da ke Mairuwa a karamar hukumar Faskari ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isa, shi ne ya tabbatar da sakin su da yammacin ranar Asabar a wata sanarwa, da ya fitar, a Katsina.
Matasan, masu shekaru tsakanin shekaru 16 zuwa 21, an yi garkuwa da su ne a gona kwanaki biyar da suka gabata.
Sai dai SP Gambo Isan bai bayyana ko an biya kudin fansa kafin sakin su ko kuma ba a biya ba.









































