Mutane biyar sun jikkata sakamakon tashin Bam a Taraba

Taraba Map
Taraba Map

A daren ranar Juma’a ne aka samu tashin wani Bam a Jalingo babban Birnin jihar Taraba lamarin da ya yi sanadiyar raunata mutum biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa asamu Fashewar Bam din ne a daidai kofar mai gari inda ake sayar da Burkutu.

Ko da yake tashin Bam din na ranar Juma’a ba a samu rasa rai ba, amma dai mutane da dama sun gigice sun rasa tunaninsu.

Tashin Bam din dai na zuwa ne daidai lokacin da daukacin al’ummar kauyen ke cikin duhu sakamakon rashin hasken lantarki.

A cewar mai rahoton gidan talabijin na Channels fashewar Bam din ta farune Jim kadan bayan da wani dan kunar bakin wake ya isa mashayar burkutun ya ajiye Jakar bam din ya tafi.

Ya kara da cewa wasu dake wajen da lamarin ya faru sun ga lokacin da Dan kunar bakin waken ya je wajen, amma basu yi magana ba sai bayan abin ya fashe

Tuni dai wadanda suka samu rauni aka garzaya da su Asibiti don ceto rayukansu.

Kawo yanzu babu wanda ya fitar da wata sanarwa akan lamarin tsakanin gwamnati da Jami’an Yan sanda a Jihar.

Lamarin yazo ne bayan da aka samu makamancinsa kwanaki 3 da suka gabata a kasuwar sayar da dabbobi kusa da wata mashaya a gari Iware dake karamar hukumar Ardo-Kola a jihar.

A wancan Fashewar Bam din dai an samu asarar rayukan mutum 6 Yayin da mutum 19 kuma suka jikkata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here