Gwamnatin Kano ta ware sama da biliyan 2 don auren Zawarawa a 2025

Mass Wedding new
Mass Wedding new

Gwamnatin jihar Kano ta ware kudi naira miliyan 2 da dubu dari 500 domin gudanar da daurin auren Zawarawa karon farko a shekarar 2025 a fadin kananan hukumomin jihar 44.

SolaceBase ta ruwaito cewa gwamnatin jihar a shekarar 2023 ta gudanar da daurin auren mutane 1,800 da suka hada da zawarawa, wadanda aka kashe da sama da Naira miliyan ɗari 800.

Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi na jihar, Musa Shanono ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da kasafin kudin jihar na shekarar 2025.

Ya ce gwamnati ta yi shirin kashe Naira biliyan 91 da miliyan 32 a fannin gudanar da mulki da samar da ayyuka da kuma shirye-shirye na hidimar auren jama’a.

Ya ce, na da nufin bude kofa domin kare hakkin dan Adam tare da inganta al’umma da samar da adalci domin samun ci gaba mai dorewa tare da inganta rayuwar ‘yan kasa.

Ya ce daga cikin kudin an ware naira miliyan daya domin ciyarwa a watan Ramadan, sai kuma Naira miliyan dari tara da hamsin da biyar na kididdigar ma’aikata, da kididdigar gidaje da yara da ba su zuwa makaranta da kuma sama da naira miliyan 1 inganta hukumar ɗab’i ta jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa an kasafta sama da naira miliyan 267 domin samar da ababen more rayuwa, da buga kalandar Musulunci da tallafawa shirin Da’awah ga sabbin masu shiga addinin musulunci.

Sauran sun hada da Naira dubu dari 589 don bincike kan tsaro da inganta ayyukan yi, da magance barace-barace a kan tituna yayin da ake sa ran kashe naira miliyan ɗari 200 don siyan kayayyakin ofis, kula da babban ofishin akanta janar da dai sauransu.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa, kasafin kudin shekarar 2025 da aka amince da shi yana da jimillar sama da Naira biliyan 719 wanda ke nuna karin sama da Naira miliyan 170 kwatankwacin kashi 31% akan abin da aka gabatar da farko na Naira biliyan 549, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika wa majalisar jiha.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here