‘Yan Najeriya bakin-haure sun shiga buya a Amurka

7c27910c 2b2a 4e74 a5e1 79a3381682fc.png

‘Yan Najeriya da ke zaune a Amurka ba da izini ba sun bayyana cewa yanzu sun takaita zirga-zirgarsu zuwa wuraren jama’a don kada a kama su a mayar da su kasarsu.

Bakin hauren sun ce sun yi haka ne bisa karfin gwiwar da suke da shi cewa za su samu kariyar fitar da su daga kasar daga tarin karar da ake shigarwa a kan Shugaba Donald Trump game da shirinsa na korar baki.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu daga cikin bakin da suka tattauna da ita sun bayyana cewa sun daina zuwa aiki da coci da sauran wuraren haduwar jama’a tun bayan da aka rantsar da Trump a matsayin shugaban Amurka na 47, don gudun kada a kama su a fitar da su daga kasar.

Kamar yadda kididdigar hukumomin Amurka ta nuna akwai ‘yan Najeriya kusan 3,690 da ke fuskantar fitar da su daga kasar ta Amurka.

Mexico ce ke kan gaba da yawan wadanda za a fitar inda take da 252,044 ,sai kuma El Salvador wadda take da bakin hauren a Amurka har 203,822.

Takardun hukuma sun nuna cewa zuwa watan 24 ga watan Nuwamba na 2024 akwai bakin haure 1,445,549 da za a fitar daga Amurkar.

Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta yi barazanar gurfanar da duk kananan hukumomi ko gwamnatocin jiha da suka ki bin umarnin Shugaba Trump din na korar bakin haure.

Tun bayan da aka fara amfani da umarnin an mayar da bakin haure 538 kasashensu daga 23 ga watan Janairu.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here