An kama wani ma’aikacin banki mai suna Kamaluddeen Lawal tare da wasu ‘yan kasuwa uku da laifin yin wani wasa mara kyau na amfani da kudin Naira a jihar Kano.
Jami’an hukumar EFCC, a Kano sun kama ma’aikacin bankin da wasu mutane uku masu suna Ismail Ibrahim Ilu da Lamido Bala da kuma Abba Mohammed.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a hanyar Unity Road da ke Kantin Kwari a Kano, biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan wasu mutane da ake zargi da safarar makudan kudade a cikin tsabar kudi.
Karin labari: Hukumar DSS ta kama masu fataucin yara a Kano
Sanarwar ta ce, wadanda ake zargin sun kware wajen karbar kudaden Naira daga bankuna daban-daban da nufin cire wasu ‘yan kudade.
Sanarwar ta kara da cewa, an kwato jimillar kudi naira miliyan bakwai da dubu dari biyar daga hannun wadanda ake zargin a lokacin da aka kama su.
EFCC ta ce za’a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.